'Ƙasurgumin dillalin ƙwaya ya shiga hannu a Brazil'

Luiz Carlos da Rocha Hakkin mallakar hoto POLICIA FEDERAL
Image caption 'Yan sanda sun ce Luiz Carlos da Rocha na rayuwa da wani sunan ƙarya bayan ya yi fuskarsa tiyatar kwaskwarima

Rundunar 'yan sandan Brazil ta cafke wani ƙasurgumin dillalin ƙwaya da ya yi ƙaurin suna a yankin Amurka ta Kudu bayan ya shafe tsawon shekara 30 yana gudun kamu ta hanyar ɓad da kama.

Ana jin Luiz Carlos da Rocha wanda ake yi wa laƙabin White Head shi ne ke jagorantar harkokin sarrafa hodar iblis a dazukan Bolivia da Colombia da Peru.

Kafin dubunsa ta cika a ƙasar Brazil, an yi wa Carlos da Rocha kwaskwarimar aikin likita a fuska da nufin ɓad da sawu a wajen 'yan sanda.

'Yan sanda sun ce an yanke wa Rocha hukunce-hukuncen ɗauri da suka haura tsawon shekara 50 a gidan yari.

Suka ce shi "wani mai aikata laifi ne da ke rayuwa cikin hattara da kuma laɓe-laɓe".

An kama Rocha ne a Sorriso, cikin jihar Mato Grosso da ke yammacin Brazil, a ranar Asabar, in ji sanarwar 'yan sanda.

Haka kuma an kama ɗaya daga cikin manyan masu haɗa baki da shi a ɗaya daga cikin sumame 24, da jami'an tsaron Brazil 150 suka ƙaddamar.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An gano akwatunan maƙare da kuɗi da bindiga gami da sauran kayayyakin Rocha yayin samamen

Haka kuma an ƙwace ƙiyasin dukiya da ta ƙunshi motoci da jirgin sama da gida ta dala miliyan 10.

Wakilin BBC ya ambato 'yan sanda na cewa Luiz Carlos da Rocha na amfani da wani dan ƙaramin jirgin sama don safarar ƙwaya daga ƙasashe maƙwabta, inda ake jigilarsu a cikin wasu rufaffun manyan motoci ana kai wa gungun tsageru a biranen Rio de Janero da Sao Paolo."

Labarai masu alaka