Syria: 'Za a kai marasa lafiya asibiti a Damascus'

Motar daukar marasa lafiya
Image caption Kungiyar agaji ta Red Crescent ta wallafa hoton motar daukar marasa lafiya na jiran daukar yaran zuwa asibiti, a shafukan sada zumunta na internet

Jami'an agaji da ma'aikatan sa kai na Syria sun fara kwashe marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali daga wani yanki da 'yan tawaye ke iko da shi a kusa da birnin Damascus.

Ma'aikatan agaji na kasashen waje sun roki shugaba Basharul-Assad na Syria ya taimaka dan a kwashe wasu yara bakwai da ke cikin mawuyacin hali da kuma su ke dauke da cutar Cancer.

Kungiyar agaji ta kasashen larabawa wato Red Crescent ta wallafa wasu hotuna a shafin tweeter na wasu yara da iyayensu cikin yanayi na rai kwa-kwai mutu kwa-kwai, su na jiran a kwashe su zuwa asibiti a birnin Damascus.

Mai magana da yawun kungiyar Red Cross a Geneva, Anastasia Isyuk ta ce babu wasu bayanai da aka yi na karin haske kan lamarin.

Sai dai ta ce tabbas an cimma matsaya tsakanin wadanda ke rikici da juna, kuma halin da marasa lafiya ke ciki a yankunan da 'yan tawaye suke iko da shi ya munana.

Babu isasshen abinci, ko ruwan sha ko magani a asibitocin da ke yankin Ghouta. Tun a farkon wannan shekara ne 'yan tawaye da ke yaki da shugaba Assad suka karbe iko da garin wanda ke kusa da birnin Damascus.

Sama da shekara 5 kenan da fara yakin na Syria, bayan guguwar juyin-juya hali ta kada a kasashen gabas ta tsakiya inda ta kawo karshen mulkin wasu daga cikin shugabannin kasashen yankin wasu kuma aka hallaka su, kamar Mu'ammar Gaddafi na Libya, da Saddam Hussain na Iraqi.

Labarai masu alaka